Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce jam’iyyarsa na da kyakkyawar damar yin nasara a zaben baɗin dake tafe.
“PDP tana da damar lashe zaben shugaban kasa kasancewar ta daya daga cikin tsofaffin jam’iyyun siyasar kasar.”
Atiku Abubakar ya shaida wa manema labarai hakan, bayan kaddamar da ofishin yakin neman zabensa a Gombe.
KARANTA ANAN: Bani Da Wani Gilla A Zuciyata Dangane da Shugaba Buhari – Gwamna Ortom
Ya ce jam’iyyar tana da dimbin goyon baya a jihar Gombe kuma za ta yi amfani da wannan damar wajen ganin an samu nasara a zaben 2023.
Ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar da su guji kamfen na zage-zage, su mayar da hankali kan yakin neman zabe da ya shafi batun nasara domin a samu karin magoya baya.
Ziyarar ta ranar Asabar a jihar Gombe ita ce karo na uku da Atiku Abubakar ya je jihar a shekarar 2022 kan harkokin siyasarsa.
A wani labarin kuma: Dole Kowace Jam’iyya Ta Faɗi Hanyar Da Ta Sami Kudin Kamfe – INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce dole ne jam’iyyun siyasar kasar nan su bayyana hanyoyin da suka samu kudaden yakin neman zabensu tare da kiyaye ka’idojin da suka shafi kudaden yakin neman zabe da kayyade kashe kudade.
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wata hira ta musamman da yayi da gidan talabijin na Trust TV.