Tsohon dan wasan Newcastle Alan Shearer ya goyi bayan Arsenal ta lashe kofin Premier bana. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ya yi imanin Gunners za ta lashe gasar kambun kan abokan hamayyarta Manchester City kuma za ta sake zama zakara a karon farko cikin kusan shekaru 20.
KU KARANTA: EFCC Ta Kwato Naira Miliyan 900 Na Shirin NHIS
Arsenal ta doke Aston Villa da ci 4-2 a ranar Asabar, inda ta koma saman teburin gasar Premier, yayin da Manchester City ta kasa doke Nottingham Forest.
Da yake tattaunawa game da wasannin karshen mako, an tambayi Shearer don hasashensa kan gasar cin kofin Premier.
“Ina tsammanin su (Arsenal) za su yi, da gaske wajan lashe gasar,” in ji shi.
Da yake magana game da wasan Arsenal na jiya, gwarzon gasar Premier ya ce, “Bisa na biyu, Arsenal ta cancanci maki uku a yau.”
A wani labari kuma, NPFL: Kester Ba Zai Yi Karawar Shooting Stars Da Akwa United Ba
Dan wasan tsakiya Shooting Stars na Ibadan , Kelly Kester ba zai buga karawar da kungiyarsa za ta yi da Akwa United a gasar Firimiyar Najeriya a yau a filin wasa na Lekan Salami dake garin Adamasingba ba, saboda rauni.
Tsohon dan wasan tsakiyar Akwa United ya bayyanawa DAILY POST cewa a halin yanzu yana jinyar rauni a gwiwarsa.