Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da aniyarta ta fara sarrafa taki daga kamfani dake zama mallakin Gwamnatin jihar.
Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamnatin ta kaddamar da shirin saida taki a farashin gwamnati a Jihar.
Cikin hirarsa da Jaridar Dimokuradiyya, Mai baiwa gwamnan jihar Bauchi shawara kan yada labarai da sadarwa Kwamared Mukhtar Gidado, ya ce tuni har gwamnatin ta kammala siyo sinadaran sarrafa takin don wadatar da jihar.
Mukhtar Gidado ya ce takin da gwamnatin ta kaddamar a jihar a makon da ya gabata ta siyo shi ne daga hannun gwamnatin tarayya, wanda kuma farashinsa ba zai zama daidai da na jiha ba.
Mai baiwa gwamnan shawara ya kara da cewa lura da irin wannan wahala ne ya sa gwamnan jihar Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya sha damarar ganin sai an fara sarrafa takin mallakin jiha don sayar da shi wa al’umma cikin rangwame.