Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shaidawa shugabannin jam’iyyar APC cewa yana da Yaƙinin cewa manufofinsa za su sa ƴan Najeriya su mayar da jam’iyyar kan karagar mulki a shekarar 2023.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin sabon shugaban jam’iyya mai mulki ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a fadar gwamnati da ke Abuja.
Wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar, ta ce Buhari ya shaida wa shugaban jam’iyyar cewa idan aka yi la’akari da manufofinsa a cikin shekaru bakwai da suka wuce, ƴan Najeriya za su yi tsalle a duk wata dama ta sake zabar APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda sun kuɓutar da mutane 12 da a kai garkuwa da su a Kogi
“Lokacin da na yi tunani a kan manufofin gwamnati a kan tattalin arziki da kuma musamman a fannin bunkasa noma, samar da ababen more rayuwa, ICT da kirkire-kirkire da kuma matakan jin dadin da muka sanya wa mata, matasa da marasa galihu a cikin al’umma, na samu sabon kwarin gwiwa cewa ’yan kasarmu za su ci gaba da marawa APC baya a yakin zabenmu,” inji Buhari.
Buhari ya kuma yi alkawarin inganta Najeriya kafin mika mulki ga gwamnati mai zuwa, inda ya kara da cewa manufofin gwamnatinsa da shirye-shiryen gwamnatinsa ba komai ba ne, illa ci gaban al’umma.
A halin da ake ciki, shugaban ya yi amfani da wannan damar wajen jinjinawa kwamitin riko da babban kwamitin tsare-tsare na babban taro karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni.