By Abbas Yakubu Yaura
Aljeriya ta zargi babbar abokiyar hamayyarta Maroko da kashe wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a kan wata babbar hanyar hamada, yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin kasashen dake makwabtaka da yankin yammacin Sahara da ake takaddama a kai.
“An kashe ‘yan Algeria uku a wani harin dabbanci da aka kai kan manyan motocinsu”, in ji fadar shugaban kasar Aljeriya, a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na APS ya rawaito.
An ba da rahoton cewa suna tafiya ne tsakanin Nouakchott babban birnin Mauritaniya arewa maso gabas zuwa birnin Ouargla na Aljeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Abubuwa da dama na nuni da cewa sojojin mamaya na Moroko a yammacin Sahara sun yi wannan kisan gilla na matsorata da wani makami na zamani. “Kisan nasu ba zai tafi a banzan ba tare da hukunta su ba.”sai dai kasar Maroko ba tace uffan ba kan faruwar wannan zargin.
Yammacin Sahara dai kashi 80 cikin 100 na karkashin ikon Maroko ne, wanda ke kallon a matsayin tsohuwar mulkin mallaka ta kasar Spain, mai arzikin sinadarin fosfat, wanda kuma take kusa da ruwan tekun Atalanta wanda yake da kifaye a matsayin wani muhimmin yanki na kasarta.
Sai dai a watan Nuwamba kungiyar Polisario ta ayyana tsagaita bude wuta bayan da sojojin Morocco suka fasa shingen kan hanyar shiga kasar Mauritania, lamarin da kungiyar ‘yan cin gashin kanta tace an gina tane daya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
An kai rahoton kashe-kashen ne a ranar Litinin, sai dai ba a samu cikakken bayani ba, kuma babu wani karin haske daga Algiers ko Rabat.
Amma Akram Kharief, editan gidan yanar gizon tsaron Mena na Aljeriya, yace “An kashe musu motocin Aljeriya a Bir Lahlou”, a kan wata babbar hanya mai tsawon kilomita 3,500 (wanda yakai mil 2,200) da ta ratsa ta yankin yammacin Sahara dake karkashin ikon Polisario.
Sanarwar da Aljeriya ta fitar ba ta bayyana irin makaman da aka yi amfani da suba, amma a watan Satumban daya gabata ne kasar Maroko ta kai daukin jiragen yaki mara matuki na Bayraktar da Turkiyya ta kera, a cewar Far-Maroc, wani shafin yada labarai na soji mai zaman kansa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa al’amura a yankin yammacin Sahara sun yi matukar tabarbarewa a cikin shekarar data gabata.A ranar Juma’a kwamitin sulhu na MDD ya yi kira da a sabunta shawarwarin zaman lafiya, a wani kuduri da Aljeriya ta yi Allah wadai da “marasa daidaito na asali”.