Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bi sahun jerin dubun-dubatan yan Najeriya da suke alhinin rasuwar tsohuwar Ministar harkokin mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan.
Da Yammacin yau Juma’a ne dai Allah Ya yi cikawa wa tsohuwar Ministar bayan fama da wata gajeruwar rashin lafiya.
Cikin sakon da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kaduwar sa matuƙa bisa jin labarin rasuwar Hajiya Aisha, inda ya ce sa’o’i kaɗan gabannin rasuwer ta sai da ya kira ta a waya, sai ba ta samu dauka ba.
Ya ce kamar yadda ya saba lokaci-lokaci yana tambayar lafiyar ta a matsayin su na aminan juna a siyasa, to amma lamarin na yau ya sha banban domin ya kira wayar ta ba ta samu dauka ba.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana marigayiyar a matsayin Jajirtacciya kuma hazikar yar siyasa da ta kafe kan gaskiya a al’amuran ta.
Hajiya Aisha Alhassan ta kasance gawurtacciyar yar siyasa ce a Najeriya wacce ta kasance Ministar harkokin mata karkashin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani ta yi murabus bayan shafe tsawon shekara uku tana mulki.