Babban Alƙalin Alƙalai na kotunan Shari’ar addinin Musulunci dake jihar Kano Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, ya amince da sauyin wurin aiki da aka yiwa wasu Alkalan manyan kotunan shari’ar addinin Muslinci da kuma na kananan kotunan shari’ar Muslunci su 9.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takadda mai dauke da sa hannun Daraktan kotunan shari’ar addinin musulinci Muhd Aminu Ibrahim, wadda kakakin kotun shari’ar addinin musulinci na jahar Kano Muzammil Ado Fagge ya rabawa manema labarai a birnin Kano.
KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Kotu Ta Soke Takarar Wani Dan Takarar Gwamnan APC
Sanarwar ta ce Wadannan sauye sauye sun fara aiki ne nan ta ke, kuma ana umartar kowanne Alkali da ya hanzarta bin wannan umarni da zarar ya sadu da takaddar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Alkalan da suka samu sauyin wajen aikin sun hada, Alkali Isma’il Garba Inuwa ya da samu sauyin wajen aikin zuwa babbar kotun shari’ar addinin musulinci ta Durbundai.
Sai Alkali Munzali Tanko da ya samu sauyin daga Rogo zuwa babbar kotun shari’ar addinin musulinci ta Sumaila, sai Alkali Ali Jibrin Danzaki daga babbar kotun shari’ar musulinci Sumaila zuwa Rogo, Alkali Halhalatu K. Zakari daga babbar kotun shari’ar muslinci ta Danbatta zuwa Rijiyar Zaki, sai Alkali Umar Sunusi Danbaba daga babbar kotun shari’ar musulinci ta Durbundai zuwa Danbatta.
Sauran sune Alkali Shamsi Ma’u’ainaini A. daga kotun shari’ar musulinci ta Dawakin Kudu zuwa Garko sai Alkali Munzali Idris Gwadabe daga kotun shari’ar musulinci Wudil zuwa Danbare, da Alkali Kabiru Ibrahim Kurawa da ya samu sauyi daga Gaya zuwa Warawa wanda kuma zai ci gaba da rike kotun musulinci dake garin Gogel sai kuma Shamsideen S. Abdullahi daga Warawa zuwa Wudil da kuma ci gaba da rike kotun shari’ar da ke Gaya.
A karshe sanarwar ta ce a guji yin wani aiki bayan saduwa da wannan sanarwa dan gujewa sabawa kalandar aikin.
A wani labarin kuma: Tinubu Zai Mulki Najeriya Na Tsawon Shekaru 8 – Gwamnan Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, zai mulki Najeriya na tsawon shekaru takwas.
Ya kuma ce babu wani dalili da zai sa a kwatanta dan takarar shugaban kasan da na jam’iyyar Labour, Peter Obi.