• A gobe Litinin ne Alkalin alkalan zai nada sabbin alkalan na Kotun daukaka Kara a Nijeriya.
• Sabbin alkalan da za’a nada sunfito ne daga sassa daban daban na kasar nan.
• Daga cikin Alkalai 18 din har da Wanda ya tsare tsohon Gwamnan Fulatu dana Taraba.
Alkalin alkalan kasar man Mai’shari’a Ibrahim Muhammad zai rantsar da wasu sabbin alkalai a Kotunnan dauka-ka Kara, guda goma sha takwas a gobe Litinin.
Acikin alkalan 18 din, akwai Mai’shari’a Adebukola Banjoko daga jihar Ogun, Wanda shine ya ya tsare tsofaffin Gwamnonin biyu, wato Joshua Dariye na jihar Fulatu, da Reverend Jolly Nyame na jihar Taraba, wanda shari’ar ta Kai har zuwa Kotun Kolin kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu yan kungiyar Hakika sun yi wa matar aure ciki
Sauran 17 da za’a nada akwai Mai’shari’a Muhammed Danjuna daga jihar Niger, Muhammad Ibrahim Sirajo daga jihar Filatu, Abdul-Azeez Waziri daga Adamawa, Yusuf A. Bashir daga Taraba, Usman A. Musale daga Yobe, Ibrahim Wakili Jauro daga Yobe, Abba Bello Mohammed daga Kano, da kuma Bature Isah Gafai daga jihar Katsina.
Sauran Alkalan da za’a nada akwai: Danlami Zama Senchi daga jihar Kebbi, Mohammed Lawal Abubakar daga Sokoto, Hassan Muslim Sule daga Zamfara, Kenneth Ikechukwu Amadi daga Imo, Peter Oyinkenimiemi Affen Bayaelsa, Sybil Onyeji Gbagi daga Delta, Olasunbo Goodluck daga Legas, Olabode Adegbehingbe daga Ondo, da kuma Bola Samuel Ademola Shima daga jihar Ondo.