Gwamnan Jihar Abia Dakta Okezie Ikpeazu ya ce al’ummar Jihar musamman na mazabarsa ne za su fayyace matsayin siyasar sa a shekarar 2023.
A shekarar 2023 ne dai wa’adin Ikpeazu zai kare a Kujerar Gwamna, kuma ala tilas ya mika ragama ga magajinsa wanda zai fito daga daya daga mazabun sanata uku na Jihar.
Majiyoyi da dama sun ruwaito cewa magoya bayan Ikpeazu na ci gaba da nuna muradinsu tare da tursasa shi fitowa takarar Sanatan mazabar Abia ta Kudu.
Yayin da aka tunkare shi dangane da alkiblar siyasarsa, Ikpeazu a yau asabar ya bayyana cewa hukuncin da yan mazabarsa suka yanke shine nashi.