Wata amarya ta rigamu gidan gaskiya kwanaki kaɗan bayan tayi aure.
Angon amaryar mai suna Idris Elmustapha Daja, shine ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin sa Facebook. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Bidiyo: Yadda wata amarya ta kama ango da duka ana tsaka da bikin su
El-Mustapha Daja ya auri amaryarsa mai suna Maryam Muhammad Liman, a ranar 6 ga watan Janairun 2023, inda ta amaryar ta rigamu gidan gaskiya a ranar Laraba 18 ga watan Janairun 2023.
An yi jana’izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanada a gidan Hajiya Fatima Madugu, dakw akan hanyar Okada, cikin birnin Minna da safiyar ranar Laraba.
Sannan aka kai ta a makwancinta na gaskiya a maƙarbartar Gbakungu cikin birnin na Minna.
“Innalillahi Wainna Ilaihir Rajiun. Kwana sha ɗaya da aure, yau na rasa ta. Allah ya jiƙan ki da rahama ya sanya aljannah Firdausi ta zama makoma a gare ki.” Idris ya rubuta a Facebook.
Matar Data Turo Maƙudan Kuɗi Daga Ƙasar Waje,Ta Dawo Ta Tarar Ɗiyarta Tayi Bushasha Da Su
A wani labarin na daban kuma, wata mata ta shiga damuwa bayan ɗiyarta ta ƙarar mata kaf da kuɗaɗen da ta riƙa turowa lokacin tana a ƙasar waje.
Wata mata mai suna Jane Wambui Mburu, ta kwashe shekaru tara tana fafutuka a Saudiyya domin ganin ta samarwa da kanta, ɗanta da budurwar ɗiyarta Hottensia Wambui, mai shekara 25, ingantacciyar rayuwa.
A cikin wannan lokacin matar mai shekara 42 a duniya, ta bar ɗiyarta ɗaya tilo domin ta kula da ƙaninta sannan ta kama musu hayar gida a garin Kiambu, na ƙasar Kenya