Kwamishinan Wasanni da Kyautata Jin daɗin Jama’a na Jihar Katsina Alhaji Sani Aliyu Danlami, yayi addu’a akan Allah ya bayyana duk wani mai sa hannu ga ta’addanci a Jihar.
Alhaji Sani Aliyu Danlami na magana ne a lokacinda yake mika kayan abinci ga wadanda harin yan bindiga ya shafa a Kauyen Yangayya dake a Karamar Hukumar Jibia.
Kamar yadda kwamishina Danlami ya bayyana cewa, ba son gwamnati bane ta rika bayar da irin wannan tallafi, illa iyaka bukatar ta a samu wanzuwar zaman lafiya a cikin Al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta yanke hukuncin zaman gidan yari na watanni 6 zuwa 9 saboda yin kwaikwayon masu sarauta,
Ya Mika sakon jajantawar Gwamna Masari ga Al’umar yankin tare da addu’a akan Allah SWT ya Kare sake afkuwar irin wannan lamarin.
Yace ƴan bindiga a jihar sun dauki wani salo na kisa, saboda halin ƙaƙa ni kayi da suka shiga sakamakon dokar daƙile matsalar tsaro da aka sanya a jihar.
Ya bukaci jama’a akan su ƙara jajircewa wurin addu’a ga jami’an tsaro wurin yaki da ƴan ta’addan.
Alhaji Sani Aliyu Danlami yace Gwamna Masari ya bayar da umarni ga Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta jiha, akan tayi ƙididdiga na gidajen da ƴan bindigar suka ƙone a yayin harin domin bada agajinda ya dace.
A nasu jawaban,Shugaban Mulki na Karamar Hukumar da Mai garin ƴangayya sun yabawa Gwamna Masari akan ɗaukin gaugawa da ya kawo ga wadanda harin ya Shafa.