Allah ya yiwa mahaifiyar mai martaba Sarkin Hadejia, Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje CON rasuwa. Ta rasu da safiyar yau Lahadi a Fadar Hadejia.
Gidan Rediyon Sawaba FM 104.9 Hadejia dake jihar Jigawa ne ya tabbatar da hakan, inda suka bayar da sanarwar cewa za a yi janai’izarta ne da misalin karfe 9 na safen yau.