Hajiya Binta Umar, Uwargidan Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar ta rasu a ranar Juma’a a garin Daura tana da shekara 70 a duniya bayan ta yi fama da rashin lafiya.
Malam Usman Ibrahim, wanda shi ne Sarkin Labaran Daura shi ne ya tabbatar da rasuwar Marigayiyar a garin na Daura dake jihar Katsina.
Inda ya ce Hajiya Binta ta rasu da misalin karfe 8 na safe a ranar Juma’a a fadar Sarkin, kuma tuni aka bizne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ibrahim ya ce Babban Limamin Masallacin Daura, Malam Suleiman Salisu shi ne ya jagoranci jana’izar.
Marigayiyar ta rasu ta bar mijinta da ‘ya’ya shida kuma jikoki tare da wadanda take riko.
Ya zuwa yanzu dai tuni gwamnatin jihar ta rufe garin na Daura ruf a wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus.