Bayanan da yake shigowa Dimokuradiyya na nuni da cewa; Allah ya karbi ran tsohon Alkali na jihar Neja kuma Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Lemu.
Iyalinsa ne suka tabbatar da rasuwarsa. Inda suka bayyana cewa; ya rasu ne da safiyar yau Alhamis.
Nuruddeen Lemu, shi ne ya bayyana hakan a madadin iyalin, inda ya ce za su sanar da lokacin yi wa mahaifin na su jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.