Allahu Akbar, Haka lamarin Allah yake.
Idan baku manta ba, a wasan Portugal da Serbia Cristiano Ronaldo yaci kwallo mai kyau amma mai kula da wasan (Refree) ya hana kwallon.
Ronaldo ya fusata nan take ya cire abun kaftin din sa ya wurgar, ya fita filin.
Sai wani yazo ya dauke shi, ya sayar dashi akan farashin $75,000 wanda yayi dai-dai da miliyan talatin da dubu dari tara da dari bakwai da hamsin #30,900,750.00 kudin Najeriya.
Sai ya biya kudin da akayi ma wata yarinya aiki.