Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Tanko Almakura ya Ƙaryata rahotannin dake yawo cewa hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta kama shi da mai dakinsa.
Da ma dai an yi ta yamadidin cewa hukumar ta cafke shi da matarsa ne bisa zargin ruf-da-ciki da dukiyar al’umma, to sai dai ya ce labarin kanzon kurege ne.
Da yake jawabi wa manema labarai ranar Alhamis, Almakura ya ce hukumar ta gayyace shi ne ta ji ta bakinsa game da zargin da ake yi masa kan wadaka da kuɗin talakawa.
Almakura wanda ke wakiltar Nasarawa ta tsakiya a majalisar datijjai, ya ce an kirkiro da wannan labari ne kawai don shafa masa kashin kaji.
Ya ce EFCC ta gayyace shi tun kafin babbar Sallah ce da ta gudana a baya bayan nan, amma ya nemi Alfarma sai vayan Sallah kuma hukumar ta amince da hakan.
Tsohon gwamnan ya kuma ce tuni ya bada duk bayanai da jami’an EFCC suka bukata, inda ya ce kuma gayyatar ba ta da wata alaka da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar APC a matakin kasa.
Daga karshe ya cf shi ma mai biyayya ne ga Jam’iyyar APC don haka ba zai yi riga malam masallaci ba wajen ayyana kudirinsa na tsayawa takarar.