An bukaci Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da yayi dubi kan irin Mummunan Hali da Titin Biyyah dake Gundumar Rigasa cikin Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna ke ciki.
Kiran ya fito ne daga ta hannun daya daga cikin jagororin yankin Kuma Mai gwagwarmaya da sharhi a kan harkokin siyayan jihar Abuhusna Sukuntuni.
A lokacin da yake bayyana irin Munin Hanyar da kuma matukar Lalacewar ta, Abuhusna Sukuntuni ya ce, ” Tsananin lalacewar hanyar ya sa Mota Bata iya bi kan hanyar kwata-kwata”
Ya Kuma kara da cewa hanyar ta taso ne daga Gidan Mai na Danaba dake By-Pass zuwa Daura Road na garin Rigasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Matashi ya hallaka Dan Uwanshi da Uka a Rivers
Kazalika ya ce, ” Ina yin wanna kira ne duba da irin kokarin da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i keyi akan kyaran hanyoyi da kuma Samar da wasu, a ciki da wajena jihar Kaduna, Wanda hakan ya sa Mu Al’umar Layin Bilya muke tunanin ko ya manta da mune a cikin tsare-tsaren Aiyukan da Gwamnatin sa keyi a jihar” inji shi.
“Dan Girman Allah, Muna Mika koken mu ne a gare ka, cikin Ladabi da Biyayya amatsayin ka na Uba Kuma Shugaba, da ka zo da kanka ko ka Dana kwamiti domin ganin irin Mawuyacin Hali da al’umar wannan yanki ke ciki”a cewar shi.
Idan za’a iya tuna wa dai, Al’umar garin Rigasa sun sha Miki koken su game da wannan hanyar, wacce suke amfani da ita a harkokinsu na yau da kullun, Musammamma wurin Kai mamata ga kushewar su dake Layin Bilyan.