Mazauna yankunan karamar hukumar Shiroro da ke jihar Niger sun shiga fargaba, sakamakon kwararar yan bindiga a yankin, da suka tsere daga jihar Zamfara, da wasu jihohin da ke da iyaka da jihar Niger.
Wata kungiya daga karamar hukumar karkashin Gamaryar kungiyoyin dake Shiroro wato COSA ce ta bayyana hakan, a yau Litinin, a cikin wata sanarwa da Sakataren kungiyar Barista Salis M Sabo, ya fitar a garin Minna Babban Birnin jihar.
“Labarin da ke zuwa mana shine, an samu kwararar dimbin yan ta’adda a wasu kauyuka kusa da karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su hanzarta shiga yankin domin sharewa al’umar Shiroro hawayen su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Sokoto ta rufe hanyoyin Sadarwa a Kananan Hukumomi 14
Ya ce, “‘ Yan ta’addan da aka gani a kan babura tare da Rufe fuskokin su, an yi imanin cewa, sun taso ne daga Zamfara ko wasu jihohin da ke makwabtaka Niger ta bangaren karamar hukumar Shiroro. Wannan yanayin ya haifar da fargaba a tsakanin mutanen yankin. ”
Ya lissafa garuruwan da ‘yan bindigan suka fantsama kamar haka: Galadiman Kogo, Zama, Magami, Magandam, Paleli, Iburo, Chukuba, Dnasapa duk a karamar hukumar Shiroro.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili a jihar inda ya zama doka.
Sanwo-Olu ya amince da kudirin a gidan gwamnatin jihar Legas ranar Litinin, wannan na zuwa ne kwanaki 11 bayan majalisar dokokin jihar ta zartar da dokar da ta haramta kiwo a fili a jihar.
Bayan zartar da kudirin a ranar 9 ga watan Satumba, Kakakin Majalisar, Mudashiru Obasa ya yabawa takwarorinsa bisa shakuwar da suke yi na ganin jihar ta ci gaba da bunkasa.
Batun kiwo a fili ya kasance mai daukar hankali a kasar domin ya haifar da sabani tsakanin gwamnonin kudu da makiyaya.
A wani mataki na dakile kashe kashen, gwamnonin kudancin sun yi taro a Legas a ranar 5 ga watan Yuli kuma sun cimma matsaya mai yawa kan kiwo a fili, sake fasalin Najeriya, tare da yin kira ga ‘yan sandan jihohi.Bayan taron, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudancin, Rotimi Akeredolu, ya ce gwamnonin sun amince da wa’adin da aka bayar na fitar da dokar hana kiwo a tsakanin mambobinta.