Manoma a cikin al’ummomi 15 na karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra sun fara farkawa saboda fargabar barkewar ambaliyar ruwa.
Al’ummomin na fama da bala’in ambaliya a kowane watan Agusta na kowace shekara.
Wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa da yawa daga cikin manoman sun samu lamuni daga bankunan noma kuma sun yi asara mai tsanani a bara.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban al’ummar Akili-Ogidi, Mista Micheal Chukwuse, ya ce mutanen yankin sun yanke shawarar daukar makomarsu a hannunsu.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/oyo-kansiloli-sun-dakatar-da-shugaban-karamar-hukumar-ido-adeojo-har-sai-abunda-hali-yayi/
“Idan manoman ba su kwashe amfanin gonakinsu a yanzu ba, zasu makara idan muka kai watannin Satumba da Oktoba.
“A wannan lokacin mutane za su yi ƙaura zuwa tudu kuma lokacin ambaliya ta tafi da amfanin gonar kuma ba za ku iya samun damar shiga gonakin ba,” in ji shi.
Mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da muhalli Chinedu Obidigwe, ya bayyana cewa ya kammala shirye-shiryen samar da kayayyakin agaji ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su.
Ya ce ya kuma bayar da umarnin a kai dashen bishiyu don noma mai zuwa.
“A yayin da nake magana da ku al’ummomin da abin ya shafa za su sami kayan agaji da kuma amfanin gona da za a yi noma a shekara mai zuwa kuma muna duban bayar da lamuni mai sauki da tallafi ta bankin noma don magance illar ambaliyar,” in ji shi.
Ya ce an sanar da hukumar ga da agajin gaggawa ta Kasa (NEMA) kan yadda aka fara kafa sansanonin ‘yan gudun hijirar, inda ya ce an tura jami’an lafiya zuwa yankunan domin kula da lafiyar wadanda ambaliyar ta shafa.
Har ila yau, Kwamishinan Muhalli na Jihar Anambra, Felix Odumegwu, a nasa martanin ya ce gwamnatin jihar ta fara aikin share magudanun ruwa tare da rushe gine-ginen da aka gina a kan hanyoyin ruwa.
Ya kuma ce an fara shirye-shiryen wayar da kan jama’a a wadannan al’ummomi domin su fara kaura da wuri zuwa wurare masu aminci.
Ya kara da cewa tuni hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar (SEMA) ta fara yin cudanya da NEMA don kara kaimi da kuma daukar matakai don rage yawan barnar da ambaliyar ruwan ke yi.
Ya kuma yi kira ga al’ummomin da ke kan layin kogin da su bi umarnin masana yanayi kan bala’in ambaliyar ruwan.
(DAILY TRUST)