Cikin Shirin “Kai Da Wakilinka”
Daga Zainab Garba Musa Bauchi
Idan ka debe watanni kadan a inda ake yanzu lokaci ne na yakin Neman zabe a bangaren kujerar shugaban kasa, Gwamna, ‘Yan Majalisun tarayya da na jahohi.
‘yan siyasa sun fafata wajen bayyana manufofi da Kuma tsare tsare a matsayin yunkuri na tallata kai ga masu zabe. Kawo yanzu tuni wadannan ‘yan siyasa da suka Sha rantsuwar Kama aiki suka hadu da tarin bukatun al’umma inda kuma suka shirya wa tunkarar wadannan bukatun.
Jihar Bauchi dai na daya daga cikin jihohi da ke da masu tsammanin samun sauyin jagoranci, la’akari da a karon farko a cikin tarihin siyasar jihar aka kada jam’iyya Mai ci a wa’adin farko sannan jam’iyyar adawa suka karbi ragamar mulki.
To ko menene tsammanin al’ummar jihar Bauchin ga wannan sabuwar gwamnati? Mun ji ta bakin wasu inda suka nemi da a boye sunansu.
“To a gaskiya har ga Allah ni a gani na yanzu ba abinda muke bukata sama da ayi Mana abubuwan da talaka zai Mora ba” a cewar daya daga cikin su.
Inda dayan ya kada Baki yace ” a nawa bangaren bai wuce addu’ar Allah yasa wannan gwamnati ta cika Mana alkawuran da ta dauka ba tun daga kan karasa hanyoyi ya zuwa biyan kudin Gratuti da Kuma ababen more rayuwar al’umma”.
Samun nasarar cimma burin da aka Sanya a gaba Yana tabbata ne da hobbasar dukkanin masu ruwa da tsaki a wajen ganin an anfani gudunmawa, a nan ne Kuma masharhanta ke ganin al’umma ba nade hannu zatayi ta zura ido ba, domin kuwa akwai muhimmiyar rawa da zata iya takawa.
Kuma a dai dai wannan gaba da ragamar ta shiga hannun zababbu, al’umma zatayi dakon ganin ko zance zai sauya zani a irin jagorancin jahar Bauchi da take muradi.
Masharhanta dai kan buga misali da siyasar Bauchi la’akari da sarkakiyar da suka ce tana dashi, Kuma wannan bai rasa nasaba da yadda al’ummar jahar ke zabe a lokacin fidda gwani ba.
To Sai dai har ila yau masharhanta na cewar Kamar al’ummar jahar Basu canki gidan ‘yan ba har yanzu duba da yadda basu karewa lafiya da wadanda suka zaba.
Wannan tunani kuwa yasa wasu ke ganin wannan gwamnati Mai ci yanzu zata Sha fama da wannan kalubale, idan akayi la’akari da yadda ta karbi gwamnati a yanayi na kwadayin ganin an kammala wasu ayyuka da suka Zama gagara badau.
Lokaci dai Shi ke Zama alkalin yanke hukunci, shine Kuma abokin tafiyar al’ummar jahar ta Bauchi.