By Abbas Yakubu Yaura
Wasu al’ummomi uku da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, wato Akilibu, Rijana da Katari sun roki Gwamna Nasir El-Rufai da kada ya sake musu matsuguni ko kuma ya share matsugunansu.
Kotu Ta Wanke Goodluck Jonathan Zai Iya Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2023
A ranar 19 ga watan Mayu, El-Rufai ya ba da shawarar sharewa tare da mayar da al’ummomin wani wuri na daban, yana mai cewa suna kusa da masu laifi da masu ba da labari.
Magaji Danjuma-Katari, shugaban al’ummomin ne ya yi wannan kira a taron manema labarai ranar Juma’a a Kaduna.
“A iyakar saninmu, al’ummominmu ba su da masaniya game da shigar kowane memba namu, kai tsaye ko a kaikaice, a duk wani lamari da za a iya tabbatar da shi na ‘yan fashi a ciki da wajen al’ummarmu.
“Don haka zarge-zargen da ake yi na cewa mu masu hada kai da ‘yan fashi ne, shirme ne, maras tushe da bare makama.
Ya ce, “Sabanin labaran da ba su dace ba daga majiyoyi masu tambaya da kuma dillalan labarai na bangare daya, mazauna wadannan al’ummomi da dama sun kasance suna fuskantar matsalar ‘yan fashi,” in ji shi.
Ya bayyana cewa akwai wata babbar hanyar shanu da ta taso daga yankin Arewa ta tsakiya kuma ta bi ta hanyar Abuja zuwa Kaduna a wani wuri da ke kusa da Katari wanda hakan ya sa ‘yan bindiga suke rika kai hare-hare.
Ya bukaci gwamnati da ta hada kai da hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, don samar da hadin kai a yaki da ‘yan fashin da akeyi a yankin.
Mista Danjuma-Katari ya kuma bukaci gwamnati da ta tabbatar da gaskiya tare da bin diddigin duk rahotannin tsaro da suka shafi al’ummomin, don tabbatar da cewa ba aikin zato ba ne.
Ya bayyana cewa duk wani dan al’ummar da aka gano a matsayin mai hada baki da ‘yan fashi da makami ya kamata a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.
Ya ba da shawarar cewa jami’an tsaron da aka tura al’umma su kasance da kayan aiki yadda ya kamata da kuma zaburar da su domin tunkarar kalubalen da ake fuskanta a lokacin.
“Dauko tare da sanya karin mambobin matasan mu cikin jami’an tsaro domin karfafa manufar aikin ‘yan sanda ta hanyar samun amincewar al’umma.
“Haɓaka matsayin ilimi na al’ummomi. A yi tanadin wani sashin ‘yan sanda domin daukar kararrakin daga karamar hukumar Chikun a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna,” inji shi.
NAN
Comments 1