Al’ummar karamar hukumar Keffi dake jihar Nasarawa a ranar Asabar 28 ga watan Satumba sun fito domin tsaftace muhalli na kowanne ranar Asabar din karshe wata da gwamnatin jihar ta ware domin tsaftace muhallan da wuraren aiki, da kasuwanni da cibiyoyi daban-daban.
Wakilin kamfanin dillancin Labaran Nijeriya, wanda ya samu halartar wuraren da aka tsaftace muhallin a karamar hukumar, ya gane wa idonsa yadda al’umma suka rika tsaftace muhallansu wanda ya hada da gidahe, shaguna da sauran su. Inda tun safiyar wannan rana shaguna suka kasance a rufe sakamakon wannan ayyukan.
Alh. Abdulrahman Maigoro, shugaban karamar hukumar, wanda ya samu zaga yankin, ya bayyana gamsuwarsa na yadda al’umma ta kowanne janibi suka fito domin ayyukan tsaftace muhallan. Ya ce hakan zai sanya a tsaftace karamar hukumar, wanda hakan zai bunkasa lafiyar al’umma.