Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Ikeja Electric Plc ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai suna Tripartite Interconnected Mini-Grid tare da Enaro Energy Limited da kuma al’ummar Ayobo dake Legas domin samar da wutar lantarki na awanni 24 ga rukunin gidaje na Ishokan Phase 1, da rukunin gidaje na MercyLand da kuma Mercy Land Phase 1 mazauna Ayobo.
Wannan shiri dai ya yi daidai da manufar hukumar kula da wutar Lantarki ta Najeriya na tabbatar da samar da ingantacciyar wutar lantarki a tsakanin al’ummomin kasar nan ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Kamfanonin rarrabawa da masu samar da wutar lantarki masu zaman kansu.
Yarjejeniyar za ta yi amfani da Mini-grid Initiative na bangaren wutar lantarki don samarwa abokan cinikayya wutar lantarki mara katsewa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Da yake jawabi yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar, babban jami’in kula da harkokin kudi na kamfanin Ikeja Electric, Seqinah Adewunmi, wanda ya wakilci babban jami’in gudanarwa, Folake Soetan, ya bayyana cewa wadannan al’ummomi za su kasance na farko da za su fuskanci wutar lantarki ba tare da katsewa ba a jihar Legas ta hanyar hada-hadar wutar lantarki na grid tsarawa da rarraba wutar lantarki.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-kashe-mutane-11-sun-sace-wasu-da-dama-a-sokoto/
A cewarta, hakan zai nuna yuwuwar abokan ciniki za su iya jin daɗin samar da wutar lantarki na awanni 24 wanda ya dace da babban aikin wutar lantarki na Ikeja, kasancewar zai samar da zaɓi a duk inda ake amfani da wutar lantarki.
Ta bayyana cewa, wannan shiri zai sa a samu manyan al’amura saboda shirin zai fadada zuwa sauran al’ummomin da ke yankin Ikeja Electric Franchise.
Manajan daraktan kamfanin na Enaro Energy, Oluwaseun Smith, ya bayyana cewa tafiyar ta fara ne kimanin shekaru biyu da rabi da suka gabata kuma ya yi farin ciki da cewa duk kokarin da aka yi na tabbatar da sanya hannu kan kwangilar ya dace.
Ya bayyana cewar kamfanin na Enaro Energy ya dukufa wajen samar da kayayyakin da ake bukata domin tabbatar da nasarar aikin.
Da yake jawabi a madadin al’ummomin, Baba Agba Lawrence ya ce duk da shakkun da aka fara yi a farkon tattaunawa kan wannan aiki, sun gamsu da irin jajircewar da Ikeja Electric da Enaro Energy suka nuna.
(DAILY TRUST)