A kalla mutane sama da dubu ashirin da biyar ne matsalar wutar lantarki ta shafa a Kasar Mozambique, inda za su ci gaba da zama cikin duhu har na tsawon wani lokaci da ba a bayyana ba.
Kamfanin dake kula da hasken wutar lantarki na Kasar ya ce Matsalar tashe-tashen hankula ne suka sabbaba wannan ibtila’i.
Wuraren da abubuwan ya fi shafa sun kunshi tsakiya da kuma Arewacin tsibirin Cabo Delgado, inda nan ne aka tarkata Kayayyyakin hasken lantarkin sakamakon Matsalar ta’addanci.
Manajan Kamfanin Hasken Wutar Lantarkin Gildo Margues ya ce za a fuskanci tsarkakiya matuka wajen gano matsalar, har a shawo kanta sakamakon irin illar da abin ya yi.