Al’ummar Osun sun dawo da ƙarfin PDP, sun karɓo Kujerar da aka sace wa Adeleke — Saraki
Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai na Kasa Bukola Saraki ya bayyana jindaɗin sa akan sakamakon Zaɓen Gwamnan Jahar Osun.
Tsohon Gwamnan Jahar Kwara ya taya murna ga Al’umma da suka tabbatar da nasarar Sanata Ademola Adeleke.
KARANTA WANNAN LABARIN: NLC Zata gudanar da zanga-zanga a dukkanin Najeriya kan dogon yajin aikin ASUU
Ɗan Takarar Jam’iyyar PDP ya doke abokin karawar sa, Gwamna Gboyega Oyetola na Jam’iyyar APC.
Saraki yayi nuni dacewar Al’umma sun sake dawowa da kujerar sa aka sace a Shekarar 2018.
“Ƙasa ta duba yadda Al’ummar Jahar Osun suka ajiye sako mai ƙarfi, wanda ke nuna cewa haske yazo.
“Munga ni, yadda Al’ummar Jahar Osun suka maido da kujerar da aka ƙwace na Abokina kuma Ɗan uwa Sanata Ademola Adeleke, wadda dama sace ta akayi shekaru 4 da suka gabata”, Ya rubuta.