By Abbas Yakubu Yaura
Shaye-shayen miyagun kwayoyi na zama babbar barazana ga kasar nan, yayin da matasa, musamman na yankin Gabashin kasar, a hankali suke ta cigaba da fama da ta’ammali da miyagun kwayoyi, wanda a baya-bayan nan, da alama ya fi shahara a tsakanin su.
Bisa la’akari da shaye-shayen miyagun kwayoyi musamman a jihar Anambra, an samu karuwar aikata laifuka da ayyukan da suka shafi kungiyoyin asiri a jihar.
Dangane da munanan ayyuka da ake samu sakamakon shaye-shayen miyagun kwayoyi, al’umma da dama a jihar sun bullo da dabarun yaki da sayar da muggan kwayoyi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Matasan al’umomi daban-daban a jihar su ma sun dauki nauyin yin mu’amala da ‘yan ta’addan dake yin sana’o’i da shaye-shayen miyagun kwayoyi.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar (UIU), Chike Odoji ya fitar, yace an haramta sayar da miyagun kwayoyi a cikin al’ummarsu.
Mista Odoji yace al’ummar za su hada kai da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) da sauran hukumomin da abin ya shafa domin kamo wadanda suka sabawa doka da suka hada da dillalan sayar da miyagun kwayoyi da masu saya.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin data gabata kan wannan ci gaban, Kwamishinan Yada Labarai da wayar da kan jama’a na Jihar Anambra, Mista C. Don Adinuba, ya ce gwamnati zata goyi bayan duk wata hanya ta doka don dakatar da shan miyagun kwayoyi a jihar.