Akalla mutum dubu 53 ne suka rasa muhallansu musamman wadanda suke kusa da duwatsun dake aman wuta a kasar Philippines a ranar Laraba.
Hukumomin kasar sun tabbatar da cewa hatsari da yankin da duwatsun ke aman wuta ba zai kare ba a nan kusa.
Aman wutar da ya auku a Taal dake yankin Batangas wanda yake kilomita 66 tsakaninsa da Kudancin Manila dake tsakiyar dutsen ya fara ne a ranar Lahadi.
Sai dai tuni hukumomi suka je suka kwashe al’ummar dake garuruwan Batangas da Cavite, sai dai har ya zuwa hada wannan rahoton wadansu al’ummar sun tsaya suna kallon dukiyarsu.
Jami’an ‘yan sanda da na soji suna daga cikin wadanda aka gani suka rage a yankin, inda wadansu kuma suka ki bin shawarar gwamnati na barin yankin, suka tsaya a yankin.