Wani ango dan Najeriya ya shayar da kowa mamaki bayan ya bar kyakkyawar amaryarsa a ranar aurensu, Legit.ng ta ruwaito.
A wani bidiyo wanda ya yadu, an ga inda fusataccen angon ya bayyana batun fasa aurensa, inda yace ba zai iya daukarta su tafi gidansa ba.
KU KARANTA: Ɗangote ta fatan ƙara samar da ayyuka ga ‘yan Najeriya 300,000
Bayan jin wannan lamarin ne ciki da alhini amaryar ta fashe da kuka inda ta bi shi da gudu tana rokonsa, amma matashin nan ya kekashe kasa yaki hakura.
Ganau sun yi iyakar kokarinsu wurin ganin sun kawo mafita dangane da wannan matsala amma abu ya ci tura.
Ya riga ya dauki matakin kenan kuma babu alamar nadama. Saidai abin ban-mamakin shi ne yadda bai bayyana dalilinsa ya yanke wannan tsatstsauran matakin ba.
Kwana Ɗaya Kafin Biki, Kayan Ango Sun Ɓace, An Sace Sadaki A Wurin Ɗaura Aure A Kano
Angon da ya nemi a sakaya sunansa ya rasa saitin rigunan da ya ajiye a wuri mai tsaro.
Lamarin da ya afku a ranar Asabar din da ta gabata ya sanya ango da iyalansa cikin rudani sakamakon yadda ya yi aiki tukuru wajen ajiye kudi da sayen wadanda suka bata.
“Yanzu me zan sa na wannan bikin sau ɗaya a rayuwa? Ya tambaya.
Wanda abin ya shafa ya kai karar lamarin ga hukumar ‘yan sanda dake Tarauni, inda suka fara bincike a kai.