Wata Amarya ‘yar Wata 6 da Aure da ke zaune a jihar Kano ta caccakawa mijinta wuka a ciki.
Matar mai suna Fatima Musa ta caccakawa mijinta mai suna Sa’eed Muhammad Hussain, wuka a cikin mai dauke da guba, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.
Yanzu haka dai Sa’eed na Kwance Rai Kwa-Kwai a Asibitin Malam Aminu Kano, da ke Jihar, Inda ya ke Karbar Magani daga Likitoci.
A daya Bangaren Dangin Fatima Musa, sun hallara cikin Asibitin Inda suka Ce Atafau ‘Yar su ba za ta aikata wannan Aika-Aikar ba.
Sai dai Wani Binkice da Wakilinmu yayi ya Nuna cewa Ba wannan ne Karon Farko da Fatima ke Yunkurin Kasheshi ba, Hasali ma Wannan ne Karo na Shida Tana Yunkurin Burma Masa Wuka domin ta Halaka shi.