A ranar Asabar, Annobar ambaliyar ruwan sama a garin Lokoja dake a cikin jihar Kogi ya shafe sama da alumomi guda 150 dake a cikin kananan hukomin tara a cikin jihar.
Kwaminshin ma’aikatar muhalli da albarkatun kasa a jihar Sanusi Yahaya ne ya sanar da hakan ga yan jarida a ranar Asabar ta wannan makon bayan kammala taron gaggawa da masu ruwa da tsaki a cibiyar hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar dake a garin Lokoja.
A cewar kwaminshinan, tuni dama cibiyar ta sanar da cewa ana tunanin annobar ta ambailiayr ruwan zata iya akuwa saboda yadda rafuka a jihar suka cika suka kuma fara yin ambaliya.
Kwaminshinan ya ci gaba da cewa, daga cikin kananan hukumomin tara da anobar ta ambaliyar ta auku duk suna a bakin rafin Riba Nija ne da kuma rafin Biniwe, inda ya ce, lamarin yafi kamari a cikin jihohi bakwai na jihar.
Aceawr sa, kanana hukumomin bakwai sune, Ibaji, Kogi Koton Karfe, Lokoja, Ofu, Ajaokuta, Omala da kuma Idah, inda ya ce, sama da kashi 90 bisa dari na alummomin dake a garin Ibaji amabaliyar ta nutsar da gidajen su.
Ya sanar da cewa, mafi yawancin alummar dake zaune a yankin nagarin na Ibaji gidajen su a kan ruwa suke kuma sakamakon ambaliyar ruwan duk sun warwastu.
A cewar sa, “ A maganar na n da nakle yi daku, ambaliyar ruwan ta hau sosai da kimanin karfe 10.60 na safiyar yau Asabar a garin na Lokoja kamar yadda hukumar kula da yanayi ta kasa NIHSA ta sanar.
Ya kara da cewa, a yan kwanunukan baya, ambailiyar ruwan ta raba jama’a daga mastugunan su.
Kwaminshinan ya kuma zayyana sunayen garuruwan da abin ya shafa da suka hadada, Adankolo, Gadumo, Egan, Budon, Kinani, Esikaku, Oreza, Edimose, Enumayi, Ogbangede, Iganumo, Bagana, Obakume, da kuma Idirisu.
Sauran garurawan kwamishina ya kara da cewa sune, Edeha, Adabode, Edegaki, Akpaku, Okpaka, Adamogu, Kasemiya, Kpakpazi, Kelebe, Ozahi, Panda, Ikumo, Irenodu, Iganumo, Geregu da sauran su.
Ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu an bude sansani sama da guda 20 a daukacin kanana hukumomin da annobar ta auku.
A karshe kwamishina ya kuma shawarci alumomin dake da gidaje a kusa da inda ambaliyar ruwan zata iaya aukuwa dasu koma zuwa sansanin da aka bude don kare rayukan su da dukiyoyin su.