Adadin wadanda suka mutu a lardin Kwazulu-Natal na kasar Afrika ta Kudu ya haura Mutum dari uku, tun bayan wani mummunan iftila’in ambaliyar ruwa da ya mamaye yankin.
Hukumomin yankin sun bayyana wannan iftila’i a matsayin Mafi Muni a tarihin kasar.
Zamtarewar kasa ta Sanya mutane da dama sun makale a cikin baraguzan gine-ginen, yayin da sauyin yanayi ke ci gaba da kasancewa Barazana ga sake samun wani ambaliyar ruwan a kasar ta Afrika ta kudu
Kazalika rahotanni sun nuna cewa aikin Ceto a yankin na fuskantar cikas,, inda wani jirgi Mai saukar angulu ke cigaba da kwashe wadanda suka yi cirko-cirko a saman gine-ginen su.
A wani labari Kuma na daban.
Tarko Ya Kama: An Cafke Ɗan Sanda na Shan Tabar Wiwi a Wurin Aikin sa
Dan sandan mai mukamin ASP, Babatunde Adebayo, ya shiga hannu ne bayan wani hotonsa da aka dauka a fakaice ya karade gari inda ya mola tabar wiwi yana kuma busa hayakinta a wurin wani taro.
A ranar Lahadi ne dai aka baza hoton hafsan dan sandan a kafofin sada zumunta, yana shan tabar wiwi, a tare da hoton aka rubuta “Hafsan dan sandan Najeriya yana shan tabar wiwi a bakin aiki a yankin Ijora, Jihar Legas.”
Wata sanarwa da Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Legas ta fitar ta ce ASP Adebayo wanda ke aiki da ofishin ’yan sanda da ke Shogunle a jihar ya shiga hannu kuma zai fuskanci hukunci bisa dokar aikin dan sanda.
Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legs, Abiodun Alabi, ya ba da umarnin a fara gudanar da bincike a kan ASP Adebayo ba tare da bata lokaci ba domin ya girbi abin da ya shuka daidai da matsayinsa.
“CP Alabi ya kuma gargadi kanana da hafsoshin ’yan sanda su guji duk wani abu na rashin da’a ko saba dokokin aikinsu, domin duk wanda aka kama zai yaba wa aya zaki,” inji sanarwar.
Comments 1