Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin kwashe mutanen Usur da Gasma da ambaliyar ruwa ta yi wa barazana a kananan hukumomin Bade da Karasuwa.
Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idi Gubana ne ya bayar da wannan umarni a ranar Lahadin da ta gabata a Gashua lokacin da ya ziyarci yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Ne Ya Fi Cancantar Zama Shugaban Kasa – Uba Sani
Ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta kwashe mazauna Usur da Gasma zuwa sabon rukunin gidaje da aka gina a Jaji Maji.
Mataimakin gwamnan ya ce sun kai ziyarar ne domin jajantawa wadanda bala’in ya rutsa da su da kuma tantance irin barnar da aka yi domin samun tallafin da ya dace.
Gubana ya kuma umurci SEMA da ta samar da kayan agaji ga wadanda abin ya shafa domin rage musu radadi.
A nasa jawabin, Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Suleiman, ya gode wa mataimakin gwamnan bisa ziyarar jajen daya kai.
Ya kuma bukaci al’ummar kasar da su yi addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.
Mataimakin gwamnan ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Alhaji Ahmad Mirwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Baba Wali da sauran su.NAN
A wani labarin kuma, Sama Da Mambobin APC 5000 Ne Suka Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar PDP A Kogi
Sama da mambobin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kogi 5000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
‘Yan jam’iyyar APC sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP ne a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar Avrugo da makwabciyarta a karamar hukumar Igalamela/Odolu a jihar Kogi.