Kungiyar Tarayyar Afrika AU, ta bai wa Afrika ta Kudu Tallafin Dala dubu Dari da Hamsin, kwatankwacin Fam Milliyan dubu Dari da sha biyar, bisa Iftila’in ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da ya afku a lardin Kwazulu-Natal.
Tun makon da ya gabata, rahotanni sun nuna cewa, ambaliyar ta yi sanadiyar mutuwar akalla sama da mutum dari da arba’in.
Kana ambaliyar ta yi janyo lalacewar ababen more rayuwa masu dumbin yawa a lardin.
Lokacin da ya ke sanar da bayar da Tallafin, Shugaban AU Moussa Faki Mahamat, ya ce kungiyar ta jaddada goyon bayanta ga kasar Afirka ta Kudu a cikin wannan mawuyacin yanayi.
A wani labari Kuma na daban.
An samu rudani a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe NAIA, dake Abuja, yayin da wani fasinja asashin gida na filin jirgin ya fado.
Fasinjan wanda ta kasance macece mai suna Mama Tobi tana wurin jirgin da za ta tashi zuwa Legas lokacin da lamarin ya faru.
Rahotanni sun bayyana cewa ta fadi sakamakon hawan jini.
Wani lauya mai suna Felix Ashimole, ya shaida wa Jaridar DailyTrust cewa fasinjan, mai fama da ciwon suga, ya mutu ne a yayin da jami’an lafiya na hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) suka ki daukar matakin a kan lokaci.
“Ina kudin da suke ikirarin an jibge ne don gyara filin jirgin sama kamar yadda duniya take? Tsawon mintuna 13 babu wani jami’in lafiya na FAAN.
“Ta mutu a hannuna da wasu mutane ‘yan kadan, wani likita a hanyarsa ta zuwa Kano ya yi kokari, amma ya kasa ceto ta.
“Amma da an cece ta da FAAN ta samar da insulin na asali. Ta kasance mai ciwon sukari. Sugarta ta hau sama; ta shiga suma; babu kulawar likita.
“FAAN da daukacin ma’aikatan jirgin da ke kasa sun yi wauta kamar ba ruwansu. Sun ci gaba da ba da sanarwar shiga jirgi amma ba su yi amfani da kakakin su ba don tambayar ko akwai wani ma’aikacin lafiya a kasa,” in ji shi.
Mai magana da yawun hukumar ta FAAN, Misis Faithful Hope-Ivbaze, ta musanta cewa FAAN ba ta mayar da martani akan lokaci ba, ta kara da cewa likitocin suna nan a wajen.
“Likitocinmu suna can. Ba mu ji dadin faruwar hakan ba.
“Mun yi nadamar faruwar lamarin, amma Allah ne mafi sani a kowane yanayi,” in ji FAAN.
Kakakin ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin.