Kwamishinan muhalli na jihar Kano, Kabiru Ibrahim Getso, ya ce dumamar yanayi da gini kan mugudanan ruwa ne yake haddasa ambaliyar ruwa a jihar dama duniya baki daya.
Dr Getso ya bayyana haka ne yayin ziyarar da yakai majalisar dokokin Kano don tattauna abubuwan da suka shafi muhalli a jihar.
Ya ce a kowace rana gwamnatin Kano tana kwashe shara fiye da tifa sittin yayin da kowane wata take kwashe shara fiye da tifa dubu daya da dari biyar (1500) a jihar nan don tabbatar da tsabtar muhalli.
Ya ce akwai bukatar bangaren zartaswa dana majalisa suyi aiki tare don dakile ambaliyar ruwan da ake samu a Kano.
Ya ce akwai kasashe da suka fi kasar nan ci gaba amma saboda canjin yanayi yasa suke fuskantar ambaliyar ruwa a bana.
KARANTA ANAN: Ka Tabbata PDP Tayi Nasara A Kano, Jigawa, Kaduna Da Neja, Saƙon Wike Ga Makarfi
Kabiru Ibrahim Getso, ya ce akwai ayyuka da gwamnati takeyi don ganin cewa ba a fuskanci ambaliyar ruwa a jihar ba ciki har da aikin tabbatar da tsaftace Kano baki daya.
Ya kuma ce a yanzu haka akwai ayyukan gina magudanan ruwa da gwamnati keyi karkashin ma’aikatar muhalli da ta ayyuka.
Kwamishinan ya ce a shekarar da muke ciki al’ummar Kano sun yashe mugudanan ruwan su fiye da shekarun baya.
Idan za a iya tunawa dai a zaman majalisar na Litinin din data gabata, ta kafa kwamitin gaggawa da zai bibiyi musabbabin ambaliyar ruwa da rugujewar gine-gine da ake samu a kasuwani da sassa daban daban na jihar nan tare da gabatar da rahoton sa nan da makonni biyu.
Tunda fari dai dan majalisa mai wakiltar Fagge Muhammad Tukur, ne ya gabatar da gudurin gaggawa dake neman majalisar tayi bincike kan musababin ambaliyar ruwan da ake fuskanta a damunar bana tare da tallafawa wadanda iftila’in ya shafa.
A wani labarin kuma: Abin Da Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Yi Don Kawo Karshen Yajin Aikin – ASUU
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta bayyana matakan da ya kamata gwamnati ta dauka domin kawo karshen yajin aikin da take yi na tsawon watanni shida.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Da yake magana a gidan talabijin na Channels cikin shirin Politics Today, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar da gaskiya.