Ambaliyar ruwa ta ƙara ɓarnata ɗimbin dukiya a garin Argungu ƙaramar hukumar Argungu dake jihar Kebbi.
Ambaliyar ta rusa gidaje da dama ta kuma tafi da dabbobi da har yanzu ba san dadinsu ba.
Wani mazaunin yankin, Malam Mansur Makama Argungu a zantawarsa da manema labarai ya ce ruwan sama ne da aka yi da misalin 12 daren Lahadi ya yi ambaliya a cikin gari da ƙauyukan Argungu.
https://dimokuradiyya.com.ng/ambaliyar-ruwan-da-ake-samu-a-kebbi-na-iya-kawo-naƙaso-wajen-samun-isasshen-abinci-a-ƙasar-nan-buhari/
Mazaunin na garin, ya ce an tsinci gawar dabbobi da suka mutu a ambaliyar, baya ga waɗanda ta yi awon gaba da su.
Yankunan da ambaliyar ta shafa a cewarsa sun haɗa da, Gwazange da Bakin Kasuwa da Gargar Iddi da Bayawa da Garkar Dogo Kafi Mari.
Ya ce jagorori a ƙaramar hukumar sun jajanta wa mutanen ciki har sanannen malamin addini na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah, Shaikh Abubakar Giro Argungu