Ruwan sama ya yi sanadin mutuwar yara biyu tare da ɓatan wani guda biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi na kwana biyu da aka kwashe ana yi a jihar Jigawa.
Ruwan saman ya yi sanadin rushewar gidaje da dama a jihar.
Alhaji Wada Faka shugaban ƙaramar Dutse ya bayyana cewa yara biyu sun rasu, sai mutane da dama da suka jikkata biyo bayan da gini ya faɗo musu a yayin ruwan saman.
https://dimokuradiyya.com.ng/ambaliyar-ruwa-ta-yi-sanadin-mutuwar-yaran-mai-unguwa-4/
Faka ya ƙara da cewa ruwan yayi wa mutane da dama ɓarna a gonakinsu, inda ya yi awon gaba da amfanin gona.
Har wayau, ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu ƙauyukan Malamawar Gangaran, Babaldu, Wurno, Kiyako, da Samamiya sun samu asara da yawa a sakamakon ruwan saman.
“Mun turawa hukumar bada agajin gaggawa ta Jigawa domin kawo ɗauki ga yankunan da abun ya shafa”.