Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce kawo yanzu sama da mutane 300 ne suka mutu a ambaliyar ruwa a fadin Najeriya a shekarar 2022.
Channels Tv ta ruwaito cewa, Darakta Janar na Hukumar NEMA, Mustapha Ahmed, ne ya bayyana hakan a wani muhimmin bita tare da masu ruwa da tsaki kan rage hadurran bala’o’i da aka gudanar a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Hukuncin Da Ya Halasta Dan Takarar Gwamnan Ebonyi
Ya ce sama da rahoto 50 ne hukumar ke karbar sanarwar ambaliyar ruwa a kullum, inda sama da al’ummomi 100 lamarin ya shafa.
A cewarsa, adadin na karuwa a kowace rana.
Ahmed ya ce ambaliyar ruwa na 2022 zai fi na 2012 muni.
A shekarar 2012, NEMA ta ce akalla mutane 363 ne suka mutu sannan sama da mutane miliyan 2.1 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa.
Shugaban hukumar ta NEMA ya zargi gwamnatin jihhohi da yin kunnen uwar shegu da gargadinta, wanda a cewarsa Zai sa rage iftila’in da kuma magance matsalolin kdake tattare da shi.
A WANI LABARIN KUMA : Ambaliyar Ruwa Ta Afkawa Gidaje 200 A Garin Makurdi – SEMA
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a garin Makurdi, kamar yadda wani jami’in gwamnati a jihar Benue ya bayyana.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Sakataren zartarwa na Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Benue (SEMA), Dakta Emmanuel Shior, ne ya bayyana hakan a garin Makurdi ranar Larabar nan a wajen rabon kayan agaji na wata-wata ga ‘yan gudun hijirar.