Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi addu’a don gujewa sake afkuwar ambaliyar ruwa da sauran bala’o’i a fadin kasar nan. Kamar Yadda Daily Post ta ruwaito
Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, a yayin bikin nadin sarauta da mika ma Sarkin Katagum na 12, Alhaji Farouq Umar sandar Girma, da fadar gwamnatin jihar Bauchi ta shirya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarkin Musulmi Ya Yi Wa Sabon Sarkin Katagum Nasiha Kan Jagorancin Al’umma
Sarkin wanda ya samu wakilcin mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya ce duk wani Iftila’i kamar ambaliya, Allah ne ya tsara shi, kuma ya kamata kowa ya amince da hakan.
Ya ce, “Mun kuma zo nan don mu jajanta wa ’yan’uwanmu da suka mutu ko kuma ambaliyar ruwa ta shafa a fadin jahar dama kasa baki daya.
Ya kara da cewa babu wani abu da kowa zai iya yi a irin wannan yanayi kamar yarda da duk wani abu da ya faru cewa daga Ugabangiji ne.
Sarkin Musulmi ya kuma yabawa Gwamna Bala Mohammed bisa gabatar da sandar girman ga daya daga cikin masu rike da tutar masarautar Usman Danfodio.
Idan za’a iya tunawa cewa ambaliyar ruwa ta shafi rayuka da dukiyoyi a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata a Najeriya.
A WANI LABARIN KUMA: Labour Party Ta Ja Kunne APC Kan Kalaman Shettima Ga Obi
Jam’iyyar Labour ta yi kira ga jam’iyyar APC da ta gargadi dan takararta na shugaban kasa, Kashim Shettima, kan kalaman da ya yi kan dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, da sauran ‘yan takara.
A ranar Asabar din da ta gabata ne jam’iyyar ta nuna rashin gamsuwarta da yadda Shettima ya yi a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar Labour, Dr Doyin Okupe
Comments 1