A yau ne ake sa ran Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphoss , zai yiwa majalisun ƙasar jawabi a kan ambaliyar ruwar da ta afku a yankin KwaZulu-Natal na kasar.
Ana kuma sa ran zai bayyana matakan da gwamnatin zata dauka da kuma karin kuɗaɗen da za ayi amfani da su bayan ya ayyana ambaliyar ruwan amastayin wani masifa a kasar.
Amma kuma bincike ya tabbatar da cewa har yanzu a kwai yankunan da basu karbi tallafi ba bayan barnar da ambaliyar ruwan tayi, inda ta mayar da dubban mutane yan gudun hijira, yayin da wasu da dama Kuma suka bata.
To sai dai shugaba Ramaphosa ya ce tuni an kebe kuɗi Dalar Amurka da yawansu ya zarce miliyan 63, amastayin tallafi, kuma za a samar da karin wasu kuɗaɗen.
Wannan dai na zuwa ne bayan da tawagar masana ta majalisar Dinkin Duniya ta ziyarci yankin a jiya Litinin domin cigaba da ziyarar aiki na kwanaki uku a yankin.
A wani labarin Kuma na daban.
2023: Allah Kaɗai ne zai zaɓi wanda zai gaje ni — Gwamna Okowa
Gwamnan Jahar Delta Ifeanyi Okowa yace a shirye yake ya baiwa Allah zaɓi ya nuna wanda zai gaje shi a shekarar 2023.
Okowa ya bayyana haka a taron Murnar zagayowar ranar haihuwa da Bada kyaututtuka na Chief Oritsetimeyin Adams a Cocin Cathedral Dake Sapele a Ƙaramar Hukumar Sapele.
Gwamnan yace baya da sha’awar ya baiwa mutane suyi zaɓi, amma ya barwa Allah ya zaɓarwa Jahar Gwamnan daya fishi wanda zai gaje shi.
Ya yabawa Cocin da Sauran Shuwagabannin ta da addu’o’i da goyon baya, sai yayi addu’a ga Allah daya zaɓarwa Jahar Gwamnan daya fi cancanta wanda zai gaje shi.
“Zaɓar wanda zai gaje Ni bawai zaɓi na bane ba, amma zaɓin Allah ne.
“Ina addu’a duk wanda Allah yake so ya zama Gwamna, Allah yasa ya zamo ya fini.
Gwamnan ya taya wanda aka shirya wa bikin ranar zagayowar haihuwar daya cimma Shekarun, sai ya buƙace shi daya maida hankali wajen yiwa Allah bauta da Al’umma baki ɗaya.