Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a garin Makurdi, kamar yadda wani jami’in gwamnati a jihar Benue ya bayyana.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Sakataren zartarwa na Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Benue (SEMA), Dakta Emmanuel Shior, ne ya bayyana hakan a garin Makurdi ranar Larabar nan a wajen rabon kayan agaji na wata-wata ga ‘yan gudun hijirar.
Ya lissafa sassan babban birnin Benue da abin ya shafa kamar Titin Naka, Achusa Kucha Utebe, Gyado Villa, Judge’s Quarters da sassan Nyiman da dai sauransu.
Shior ya lura cewa ambaliyar ba ta kasance mai muni ba a jihar a baya.
Karanta kuma: Hukumar NiMET Ta Yi Harsashen Ambaliyar ruwa A Jihohi
Ya ba da tabbacin cewa kwamitin jihar kan ambaliyar ruwa ya amince da fadada wasu sansanonin da aka zabo a Makurdi, Guma da Logo domin daukar wadanda ambaliyar ta shafa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Shior ya kara da cewa hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan wasu al’umomi a jihar ya yi sanadiyar raba mutane sama da 400,000 da muhallansu.
Ya ce gwamnatin jihar na bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa da kuma ‘yan gudun hijira daga Kamaru da ke zaune a karamar hukumar Kwande da ke jihar.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wa jihar wajen kula da ‘yan gudun hijirar, yana mai cewa nauyi na kara yi wa gwamnatin jihar yawa da ci mata tuwo a kwarya. (NAN)
A wani labarin kuma: Mutane Uku Ne Suka Mutu, An Kona Gidaje A Rikici Kan Nada Sarki A Ogun
An bayar da rahoton mutuwar mutane uku yayin da aka kona gidaje da motoci a rikicin da ya barke kan zaben sabon sarki a garin Agosasa da ke karamar hukumar Ipokia a jihar Ogun.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin.