Ambaliyar Ruwa ta hallaka Mutane 24, ta shafi Dubbai a Katsina – SEMA
Mutane 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon Ambaliyar Ruwa da iska da ta shafi mutane 18,245, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Katsina (SEMA) ta bayyana.
Kakakin Hukumar, Umar Muhammad ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Katsina ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Deji Adeyanju ya shawarci ASUU kan Matakin da ya kamata ta ɗauka akan Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara
Muhammad ya ce an samu rahoton afkuwar bala’in a daukacin Ƙananan Hukumomin jihar 34 a lokacin damina ta Shekarar 2022.
Ya ce wasu Mutane da dama sun samu raunuka daban-daban a sakamakon bala’o’in.
Kakakin hukumar ya kuma ce Ambaliyar Ruwan ta lalata gidaje 16,625 sakamakon bala’in.
A cewarsa, gonaki 1,620 kuma sun nutse a cikin Ƙananan Hukumomin Kafur, Danja da Ingawa.
Ya ce ta lalata dukiyoyi da amfanin gona da aka yi kiyasin asarar ta kai miliyoyin naira sakamakon bala’in.
Mohammed ya ce tuni hukumar ta tantance Gidaje da Gonakin da abin ya shafa domin taimakawa waɗanda abin ya shafa.
Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta fara rabon tallafin ga wadanda abin ya shafa.
Kakakin ya ce hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), nan ba da jimawa ba za ta raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.
A wani labarin kuma: An kama wani Mutum kan zargin kashe Ƙananan Yara
Rundunar Ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke wani mutum mai suna Barnabas Abduneza mai shekaru 40 bisa zargin kashe karamar yarinya.
Wani mazaunin kauyen Kpasham da ke karamar hukumar Demsa a jihar Adamawa, Abduneza, ya kai wa mamacin da mahaifiyarta hari a makon jiya, 29 ga watan Satumba a kauyen Kadamti, lamarin da ya yi sanadin mutuwar karamar yarinya da kuma mummunar rauni a jikin mahaifiyar.