Hukumar bada agajin gaggawa reshen jihar Kano SEMA ta bayyana cewa, gonaki 95 da gidaje 2,026 sun lalace sanadiyar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 8 dake jihar.
Babban sakataren hukumar Dakta Sale Jiji ne ya bayyana hakan a garin Kano, inda ya ce, hukumar hasashen yanayin ta kasa NiMet, ta yi hasashen ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 25 dake jihar, sakamakon mamakon ruwan sama da za’a samu.
“Mutane 26 sun mutu, gidaje 2,026 sun lalace, ya yin da gonakin Shinkafa 95 suka lalace, Mutum 19 kuma suka sami mummunan raunika, sanadiyar ambaliyar ruwa a jihar.
Jiji ya kuma bayyana kananan hukumomin lamarin ya shafa kamar haka; Bunkure, Minjibir, Tarauni, Daguwa, Rano, Ungogo, Tudun Wada, da kuma karamar hukumar Tsanyawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu daga cikin tallafin da Sanata Uba Sani ya bai wa Al’umar su
” Mun ziyarci karamar hukumar Bunkure, Minjibir, Tarauni da kuma karamar hukumar Doguwa, da kuma rarrabama wadanda lamarin ya shafa kayan tallafi” inji shi.
“Kayan da muka rarraba mu su sun hada da, abinci, buhunhunan siminti, kwanon rufi, tabarmi, da kuma barguna” kamar yadda ya bayyana.
A cewar shi, hukumar ta SEMA ta tura jami’an ta karamar hukumar Tudun wada, inda lamarin ya fi kamari, domin duba asarar da a ka yi. da kuma samun cikakken bayanai.
Kazalika ya ce, gwamnatin jihar ta Kano gami da ta tarayya, sun samar da wani sansanin yan gudun hijira da zai dauki Mutum akalla 700, Wanda kuma aka cikashi da kanan katifu da kuma gadaje, ga wadanda lamarin ya shafa
A karshe Jiji ya bukaci mazauna jihar, da su kai rahoton kowani iftila’i ga Shuwagabannin yankunan su. Inda kuma ya kara yin kira da su kauce wa zuba shara a magudanar ruwa.
Comments 1