Babban Daraktan Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Bauchi, Dakta Ibrahim Kabir, ya tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje 1,453 da gonaki da dama a kananan hukumomin Zaki da Gamawa.
Punch ta ruwaito cewa, Kabir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Gwamna Bala Mohammed yayin da ya kai ziyarar jajantawa al’ummar da abin ya shafa a ranar Asabar a karamar hukumar Zaki.
KARANTA WNANAN LABARIN: Mun Baiwa Yan Kasashen Waje Sama Da 200 Shedar Zama Yan Najeriya—– Gwamnarin Tarayya
Ya ce bayan tantance irin barnar da mamakon ruwan sama ya yi a ranar Laraba, an gano ya kashe mutane uku, tare da lalata gidaje 1,453 da gonakin da ba a tantance adadinsu ba a kananan hukumomin biyu.
Ya kuma ce ambaliyar ta kuma katse hanyoyin da ta hada kananan hukumomin biyu da al’ummomi da wasu sassan jihar a wurare shida a kan babbar hanyar.
Dokta Kabir ya shawarci al’ummomin da su koma wuraren da suka fi tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.
Gwamna Mohammed ya jajanta wa al’ummar yankin kan mutuwar mutane uku da lalata gidaje da gonaki a kananan hukumomin Zaki da Gamawa.
Ya yi kira da a hada karfi da karfe wajen magance munanan illolin da ambaliyar ruwa ta haddasawa al’umma a fadin jihar.
Mohammed, a lokacin da yake duba irin barnar da ambaliyar ta yi, ya ce al’ummomin sun fuskanci hatsarin ambaliya mai muni matuka.
Ya kuma bayyana cewa ana samun asarar rayuka da dukiyoyi duk shekara a jihar
Mohammed ya yabawa Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya kan yadda suke shiga cikin sauran bangarorin ci gaba da ababen more rayuwar al’ummar jihar.
Sai dai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka wa jihar wajen samar da mafita ta din-din-din a kan wannan matsala, tare da samar da kayayyakin agaji ga wadanda abin ya shafa.
Gwamnan ya mika kayan agajin tireloli guda biyu na Masara da magunguna da kayan masarufi ga kananan hukumomin Zaki da Gamawa.
A karahe Ya kuma umurci hukumar ta SEMA da ta gaggauta sayo kwale-kwale guda 14 ga al’ummar da lamarin ya shafa tare da yin lissafin barnar da ambaliyar ta yi domin baiwa gwamnati damar daukar matakai na gaba.
A WANI LABARIN KUMA: Yar Shekara 13 ta Rubuta Tare da Haddace Alqur’ani Hizufi 60
Wata yarinya ‘yar shekara 13 mai suna Zuwaira Ahmed da ke kauyen Kagara da ke karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ta haddace tare da rubuta cikakken Alkur’ani Mai Girma Izufi 60.
Da yake jawabi a wajen bikin karrama yarinyar a ranar Asabar, Hakimin Mahuta, Alhaji Bello Abdulkadir, ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba.