Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Babban Titin Lokoja, Gidajen Ruwa, Cibiyoyin Bauta
Masu ababen hawa da ke bin hanyar Lokoja-Ajaokuta, wadda ta hada wani bangare na gabacin jihar, sun makale a titin Ganaja zuwa Lokoja a ranar Litinin din da ta gabata, yayin da ruwa daga kogin Neja/Benue ya mamaye titin tare da sa ba za a iya wucewa ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani Ya Sami Tabbacin Goyon Baya Daga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna
Daily Trust ta tattaro a ranar litinin cewa motoci guda uku da suka yi yunkurin tsallakawa sun makale a kan babbar hanyar, inda wasu suka yi fakin a kan titin tare da haddasa doguwar layukan motocin da aka ajiye a gefen hanya.
Wani direban mota mai suna Malam Idris Usman wanda ya yi ikirarin cewa yana tuka Ayangba -Lokoja a kowace rana, ya ce sai da ya sauke fasinjojinsa a kauyen Ganaja-Lokoja sannan ya koma.
An lura cewa masu ababen hawa da za su je Gabas daga Arewa sai sun bi ta Okene -Adogo ta babbar hanyar Ajaokuta zuwa Itobe don ci gaba da tafiye-tafiyensu.
Fasinjoji da dama ne suka hau kwalekwale domin wucewa ta bangaren babbar hanyar zuwa daya bangaren Lokoja domin ci gaba da tafiya.
Har ila yau, gidaje da dama a rukunin Gadumo, Adankolo, Kpata da Marines da ke Lokoja da majami’u, masallatai da wuraren kasuwanci ne ambaliyar ta rutsa da su.
A halin da ake ciki, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) ta ce akalla mutane 18,406 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kananan hukumomi 14 na jihar.
Darakta Janar na hukumar Yabawa Kolo ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Maiduguri ranar Litinin.
Ta lissafa yankunan da abin ya shafa sun hada da Shani, Kwaya Kusar, Biu, Damboa, Askira Uba, Chibok, Kaga, Dikwa, Maiduguri, Monguno, Jere, Mobbar, Gwoza, Monguno da Kala Balge.
Shugaban SEMA ya ce aikin tantance barnar da aka gudanar a kananan hukumomin Monguno da Kala Balge ya nuna cewa ambaliyar ruwa ta mamaye filayen noma, inda mutane 1,735 suka rasa matsugunansu, sun lalata matsuguni 681 da bandaki 112 a sansanonin GGSS, NRC da Gana Ali.
Yabawa ya bayyana cewa kwamitin kula da ambaliyar ruwa na jihar karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Usman Kadafur, ya dukufa wajen taimakawa wadanda bala’in ya rutsa da su. (NAN)
A wani labarin kuma: Cutar Karnuka Na Kashe Ƴan Najeriya 55,000 A Duk Shekara – USAID
Cutar Karnula na kashe kusan mutane 55,000 a duk shekara a Najeriya, inda cutar ta karnuka ke da kashi 94 cikin 100 na mutane da aka tabbatar sun kamu da cutar, in ji Mieko Mckay, mataimakin daraktan hukumar ta USAID a Najeriya.
Ta bayyana hakan ne jiya a Abuja a yayin kaddamar da wani shiri na kasa don kawar da cutar kanjamau da karnuka a Najeriya wanda ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar lafiya da ci gaba ACTION – Najeriya da sauran abokan hadin gwiwa a gaba na Ranar Rabies ta Duniya ta bana.