Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a Makurdi, babban birnin jihar Benue. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Benue (SEMA), Dakta Emmanuel Shior, ne ya bayyana hakan a Makurdi ranar Laraba a wajen rabon kayan agaji na wata-wata ga ‘yan gudun hijira.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Kori Al’umomi 11 A Jigawa
Ya lissafa sassan da abin ya shafa kamar Titin Naka, Achusa Kucha Utebe, Gyado Villa, Extension na Judge’s Quarters da wasu sassan Nyiman da dai sauransu.
Shior ya kuma bayyana cewa ambaliyar ba ta yi muni ba a jihar .
Ya ce kwamitin da aka kafa a jihar kan ambaliyar ruwa ya amince da fadada wasu sansanonin da aka zabo a Makurdi, Guma da Logo domin daukar wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Ya kara da cewa hare-haren baya-bayan nan da aka kai wa wasu al’umomi a jihar ya yi sanadiyar raba mutane sama da 400,000 da muhallansu.
Ya ce gwamnatin jihar na bayar da tallafin ga wadanda abin ya shafa da kuma ‘yan gudun hijira daga Kamaru da ke zaune a karamar hukumar Kwande da ke jihar.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka domin kuwa nauyi na kara yi wa gwamnatin jihar yawa
Shior ya ce, maharan sun kashe da raunata, tare da lalata kayayyakin more rayuwa kamar kasuwanni, coci-coci, da makarantu a cikin al’umma da suka kai hari.(NAN)
A WANI LABARI KUMA: 2023: Peter Obi Ɗan Takarar Shiyya ne – Reno Omokri
Wani mai sharhi kan al’umma Reno Omokri ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a matsayin dan takarar yanki.
Omokri ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake magana a gidan Talabijin na Channels, a shirin Siyasar mu a Yau.