Al’ummar karamar hukumar Ondo ta yamma sun shiga halin kaulani bayan da ambaliyar ruwa ta hadiye wasu uan acaɓa biyu a tanar talata.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta biyo bayan mamakon ruwan sama ne da aka fara tun da misalin karfe biyar na yamma har zuwa takwas a dare.
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin sun samu nasarar ceto mutum guda, yayin da kuma aka samu gawarwakin mutane biyun da suka rasa rayukansu a karkashin gada.
Kazalika ambaliyar ruwan ta yi sanadiyar salwantar dukiya ta miliyoyin naira a ranar Talatar.
Lamarin ya kuma yi sanadiyar harzuka al’ummar yankin fitowa yin zanga-zanga don nuna fushin su bisa irin halin ko in kula da ake nunawa yankin.