Biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe kwanaki ana yi, ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje kusan 400 a wasu sassan gundumar Pilgani da ke karamar hukumar Langtang ta Arewa a jihar Filato.
DAILY POST ta ruwaito cewa yankunan da lamarin ya fi shafa sun hada da Zamadede, Shilur, Pishe, Angwan gani, Galang, da dai sauran sui.
KARANTA WANNAN LABARIN: Har Yanzu Buhari Bai Cika Ko Daya Daga Cikin Alkawuran Da Yayi Ba – Tsohon Kakakin PDP
A cewar wani mazaunin garin Zamadede, Mista Nantip, “Duk abin da muke da shi a gidanmu ya lalace.
“A yayin da nake magana, a halin yanzu sama da mutane 200 sun rasa matsugunansu sakamakon mummunan ambaliyar runwan.”
Da yake mayar da martani kan lamarin, Shugaban karamar hukumar Hukumar Langtang Ta Arewa Barr. Rimven Zulfa, ya ce, “Mun samu rahotannin ambaliyar ruwa a cikin al’ummomin kuma za mu bincika kuma mu tabbatar da cewa an tuntubi hukumomin da suka dace domin a samar da tallafi ga mutanenmu.”
Yayin da take kokawa kan lamarin, Zulfa ya ce, “Har yanzu muna kira ga mutanen da ke zaune a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa da su bar wurin, domin har yanzu hadarin ambaliya bai kare ba.”
Ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga ” walwalan” wadanda ya rike amanarsu, daidai da manufofin gwamnatin APC a jihar.
“Za mu tsara hanyoyin da za a magance ambaliyar ruwa a yankunan karkara,” in ji Zulfa.
A WANI LABARIN KUMA: Kotu Ta Kori Wani Dan Takarar Gwamnan A APC
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jalingo a jihar Taraba ta kori Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Daily Trust ta ruwaito cewa, A hukuncin da ya yanke ranar Talata, Mai shari’a Simon Amobeda ya soke zaben fidda gwani wanda ya samar da Bwacha a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a jihar.