A kalla al’ummomi goma sha biyu galibinsu a kananan hukumomin Etsako ta tsakiya da Etsako ta gabas na jihar Edo ne ambaliyar ruwa ta mamaye yayin da kogin Neja ya cika makil
Daily Trust ta ruwaito cewa, al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Udaba-Ekphei, Anegbette, Ukpeko Orle, Ofukpo, Agbabu, Osomegbe, Udochi, Yelwa, Ake Island da Ifeku Islay.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NDLEA Ta Kama Tsohon Dan Kwallon Najeriya Da Hodar Ibilis
Galibin Manoman na fama da radadin rasa amfanin gonan su a garin Etsako da ke Jihar Edo, sakamakon mamaye gonakin su da ambaliyar ruwan ta yi, wadanda suka hada da: gonakin noma shinkafa, rogo, kayan lambu, dankali, gyada da dai sauran su.
Mazauna yankin sun ce, majami’u, masallatai, kasuwanni da makarantu, duk ambaliyar ruwa ta mamaye su tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya da su kawomusu dauki.
Wani mazaunin unguwar Udaba, Mista Isaac Omoaka, ya ce ambaliyar ta fi ta shekarar 2012 muni.
Da aka tuntubi kwamishinan ayyuka na musamman na ta jihar Edo, Osasere Evboumwan, ya ce hukumomin da abin ya shafa sun ziyarci wuraren kuma suna tattara bayanai kan mummunan iftila’in
A nasa bangaren, shugaban gudanarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a Jihar Edo, Dahiru Yussuf, ya ce hukumar na tuntubar reshen ta dake yankin da abun ya shafa domin ba da rahoton yau da kullum kan abin da ke faruwa a karamar hukumar.
Dahiru ya kuma bayyana cewa, hukumar ta samar da abinci da kuma wasu kayayyaki domin taimakawa mutanen da ambaliyar ruwar ta shafa.
A WANI LAVlBARIN KUMA: Yan tawayen Tigray Sun Janye Daga Yankin Amhara
Dakarun kabilar Tigrai sun ce sun janye daga yankunan yankin Amhara na kasar Habasha da suka mamaye sama da wata guda a cikin yakin basasar da ake ci gaba da gwabzawa a arewacin kasar Habasha.
A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na yankin, ‘yan kabilar Tigrai sun ce sun sake yin la’akari da tura Dakarun su saboda akwai bukatar yin sauye-sauye domin yakar rundunar hadin guiwar sojojin tarayyar Habasha da kawayenta na Eritrea