A daidai lokacin da ake samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Mumbai na kasar Indiya da wasu yankunan da ke kusa da shi, Mamakon Ruwan saman ya yi sanadiyar lalata miliyoyin dukiyar al’umma a babban birnin kasar.
Ya yin da yankuna da dama na birnin suka cigaba da samun ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya janyo ambaliyar ruwa mai tsanani.
Kana Hukumar kula da yanayi ta kasar Indiya ta fitar da sanarwar gargadi ga birnin da kuma gundumomin da ke makwabtaka da ita, inda ta yi hasashen za a iya samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin kwanaki biyar masu zuwa.
Tawagar dake kulawa da iftila’i ta kasar wacce ta kasance runduna ta musamman da ke ba da agaji ga wadanda lamarin ya shafa, sun shiga yankunan domin aikin ceto.
Rahotanni sun nuna cewa, ana Yawan samun ruwan sama a jihar Maharashtra dake kusa da Mumbai a yan hekararun baya-bayan nan.
Sai dai Kuma masana sun ce sauyin yanayi ya sa ruwan saman ya karu sosai kuma ba a iya hasashensa a shekarun baya-bayan ba,
Kazalika dubban mutane ne ke ƙaura zuwa Mumbai a kowace rana don neman ayyukan yi wanda ke haifar da karin gine-gine a birnin, kuma yankuna da dama a kasar ba su da magudanan ruwa mai kyau, wanda hakan ke haifar da ambaliya.
Ko A ranar Talata, sabon babban ministan Maharashtra da aka nada, Eknath Shinde, ya ziyarci sashin hukumar dake kula da iftila’i a kasar, don sa ido kan ayyukan agaji da ceto, yayin da aka ga mazauna yankin suna yawo a cikin ruwa mai datti inda kuma magudanan ruwa suka cika makil, tare da cika tituna da tarkacen datti.