Ambaliyar ruwan sama ta yi ajalin mutane huɗu tare da rusa gidajen 5,200 a ƙananan hukumomin Rogo da Dambatta a jihar Kano.
Hukumar Agaji ta jihar Kano ta ce iftila’in ya yi ajalin mutu biyu tare da rusa gidaje 5,000 a ƙaramar hukumar Dambatta, da wasu biyu da suka mutu a Rogo inda gidaje 200 suka rushe.
Babban Daraktan hukumar, Saleh Jilli ya asarar ta auku ne bayan ruwa da aka tafka tare da ambaliya a ƙananan hukumomi 20 a jihar Kano.
https://dimokuradiyya.com.ng/ambaliyar-ruwa-a-anguwar-kurna-asabe-dake-jihar-kano/
“Mun tura tawagarmu domin tantance abin da ya faru muka kuma ziyarci Rogo da Dambatta domin jajantawa game da iftila’in”, inji shi.
Saleh Jilli ya ce mutanen da ambaliyar ta raba da muhallansu na tsugune a wurin dangoginsu a yankunan da abin ya shafa.
Ya ce hukumar ta raba kayan tallafi na Naira miliyan 3.5 ga mutanen da ambaliyar ta shafa domin sauƙaƙa musu halin da suka shiga.